Mutum 36 sun mutu a hatsarin mota a Kenya

Hatsarin mota a Kenya Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Adadin wadanda suka mutu ya karu daga 30 zuwa 36 bayan da shida daga cikin masu raunuka sun mutu a asibiti.

Fiye da mutum 36 suka mutu a wani mummunan hatsarin mota tsakanin wata motar fasinja da mai dakon man fetur.

Hatsarin ya auku ne da safiyar Lahadi a garin Salgaa dake kimanin kilomita 200 yamma da birnin Nairobi, inda fiye da mutum 12 suka jikkata.

A sanadiyyar wannan hatsarin, hukumar sufurin da kiyaye hatsurra ta Kenya ta dakatar da tafiye-tafiyen dare ga motocin sufuri masu dogon zango.

"Ina barci a lokacin da hatsarin ya auku, kawai naji wani kara ne da ihun mutane kafin aka taimaka aka fitar da ni." Wani fasinja kenan wanda ya tsira da ransa a wata hira da wata tashar rediyo dake yankin.

Rahotanni sun ce duka direbobin motocin sun rasa rayukansu, kuma akwai wani yaro dan shekara uku a cikin fasinjojin da suka mutu.

Hukumar kuma ta bayyana cewa hatsarin, wanda ya auku da misalin karfe 3 na dare, ya auku ne a sanadiyyar wani taho mu gama tsakanin wata motar fasinja mai daukar mutum 62 da wata tankar man fetur a wani wuri da yayi kaurin suna sabili da yawan hatsura.

Kungiyar Red Cross ta Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum 36.

Hakkin mallakar hoto AFP/Getty
Image caption Jami'ai sun ce 34 daga cikin matattun fasinjojin motar bas din ne kuma biyu na cikin babbar motar

Sauran wadanda suka sami raunuka an kai su babban asibitin garin Nakuru da wasu asibitocin dake garuruwan dake kusa.

A farkon watan Disamba, fiye da mutum fiye da 20 ne suka halaka a wani hatsarin mota a daidai wannan wurin.

Kuma hukumar sufuri da kiyaye hatsurra ta kasar ta ce ta damu da yadda ake asarar rayuka kimanin 3,000 a kowace shekara, ta a dalilin hatsurran mota a fadin kasar.

A bana kadai, mutum 2,883 ne suka halaka a a kan wannan hanyar, kuma mutum 300 a cikinsu sun mutu ne a watan nan na Disamba.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce Kenya na gaba-gaba a kasashen duniya da aka fi samun aukuwar hatsurra.

Labarai masu alaka