Nigeria: 'Harin Benue mugunta ce da rashin tausayi'

Shugaba Muhammadu Buhari
Image caption Shugaba Buhari ya ce harin na mugunta da rashin tausayi ne. da gwamnati ba za ta amince da shi ba

Shugaban Nigeria Muhammad Buhari, ya yi Allawadai da tashin hankalin da ya barke tsakanin Fulani makiyaya da Manoma a kasar, inda ya kira fadan da na tsagwaron mugunta ne da rashin tausayi.

Kalaman nasa na zuwa ya yin da daruruwan mutane suka cika titinan birnin Makurdi na jihar Benue dan nuna rashin jin dadi kan tashin hankalin.

Jami'an gwamnati sun ce akallah mutane 33 ne aka hallaka, a lokacin da Fulani makiyaya dauke da muggan makamai suka afkawa manoma kwanaki biyu da suka gabata.

Sama da shekara 10 kenan, ake rikici tsakanin Musulmi makiyaya da manoma mabiya addinin Kirista akan batun gonaki na yin kiwo.

Wasu 'yan Nigeria dai sun zargi Shugaba Bhuari da dauke ido akan rikici irin wannan, a cewarsu wai saboda shi ma Bafulatani ne.

Masu zanga-zangar kin jinin hare-haren da ake kaiwa a jihar Benue sun jefi gwamnan jihar a lokacin da ya nemi yi musu jawabi .

Shaidu dai sun ce masu zanga-zangar sun bazu cikin garin Makuridi ne domin nuna rashin jin dadinsu game da hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar ta Benue da ke tsakiyar Najeriya.

Tare da kiran shugaban Najeriya ya dakile hare-haren da ake kai wa jihar Benue din ko kuma ya yi murabus.

Gwamnatin jihar Benue dai ta ce an kashe akalla mutum 33 a hare-haren da aka kai kauyukan jihar da ke garin Guma, an kona gidaje da dama kuma mutane da yawa sun tsere daga gidajensu.

Gwamnan jihar, Samuel Ortom, dai daga garin na Guma ya fito.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Lawrence Onoja, ya shaida wa BBC cewa an fara kai hare-haren ne ranar farko ta sabuwar shekara kuma aka ci gaba da kaiwa har zuwa safiyar Talata.

Kawo yanzu dai kungiyar makiyaya ta Najeriya ba ta ce komai ba game da harin da aka daura wa makiyaya alhakin kaiwa.

A kwanakin baya ne dai gwmamnatin jihar Benue ta kaddamar da dokar hana kiwo a fili.

Wasu makiyayan sun yi na'am da dokar hana kiwo ta jihar Benue din yayin da wasu suka ki amincewa da ita.

Sama da shekara 10 kenan, ake rikici tsakanin Musulmi makiyaya da manoma mabiya addinin Kirista akan batun gonaki na yin kiwo.

Labarai masu alaka