Likitoci sun ce 'yan Afirka na mutuwa yayin tiyata

Likitoci a dakin fida
Image caption Binciken ya gano wata babbar matsalar ita ce, ta rashin kwararrun likitoci a asibitocin Afirka

Masana kimiyya sun ce adadin mutanen da suke mutuwa bayan an yi musu tiyata a kasashen Afurka, ya rubanya har sau biyu idan aka kwatanta da wasu kasashen duniya.

Ko da yake marassa lafiyar na kasancewa matasa ba kamar sauran wurare ba.

An gudanar da binciken a kasashe 25, da kuma mujallar The Lancet ta kiwon lafiya ta wallafa, inda aka gano ba a cika mayar da hankali kan marassa lafiya gabannin yi musu tiyata ba.

Sannan kuma ga rashin ingantattun kayan aikin zamani a asibitoci, sai kuma uwa uba rashin kwararrun likitoci da suka goge a fannin tiyatar inda rahoton ya ce lamarin ya fi shafar talakawa.

Sai dai masu binciken sun nuna damuwa kan yadda daidaikun 'yan Afurka ne ake musu aikin tiyata na zamani mai lantarki.

Haka kuma an gano yawan mutanen da likitoci ke sanyawa a yi wa tiyatar ya rubanya da kashi 20, idan aka kwatanta da ainahin wadanda ba sa bukatar yi musu aiki.

Masu binciken sun kira lamarin da kisan mummuke, wanda aka gano kusan shi ke janyo wa marasa lafiya mutuwa bayan an kammala tiyata.

Batun rashin kayan aiki a asibitoci a wasu kasashen Afurka dai batu ne da aka dade ana tattaunawa, ciki har da Najeriya.

Wasu masu hannu da shuni sun gwammace su niki gari har zuwa kasashen waje don neman lafiya, yayin da talakawan kasar ba su da wata dabara baya ga mika wuya.

Labarai masu alaka