Mece ce tashar ruwa ta kan tudu?

Inland dry port Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tashar ruwa ta kan tudu

Shugaba Muhammadu Buhari ya bude wata tashar ruwa ta kan tudu ta farko a Najeriya a birnin Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

Wannan tasha za ta taimaka wa 'yan kasuwar yankin arewacin kasar wajen rage wahalhalun zuwa kudancin Najeriya domin karbar kayansu ko fitar da su zuwa waje ba tare da kashe kudaden fito da na sufuri ba.

Mecece tashar ruwa ta kan tudu?

Akwai wasu tashoshin da akan gina a wasu wurare da ke nesa da tashar jirgin ruwa da ake kira tashar ruwa ta kan tudu.

Ita wannan tashar tana iya kasancewa mai nisan daruruwan kilomitoci daga gabar teku, kuma akan hada tashar gabar teku da wannan tasha ta kan tudu ta hanyar titunan mota ko hanyar jirgin kasa.

Tashar, wata cibiya ce ta hada-hadar kayan da ake jigilarsu cikin kasar.

Image caption Tashar na taimakawa wajen samar da wuraren ajiyar kaya daga jiragen ruwa cikin hanzari

Bayan wannan aikin, tashar ruwa ta kan tudu na samar da wasu muhimman wurare na ajiyar kaya da kula da na'urorin sufuri da ayyukan kwastan.

Sannan akan tsara wurin da ake gina tashar kan tudu domin ta kawo saukin cunkoson da ake fuskanta a tashar jirgin ruwa.

Kana tashar na taimakawa matuka wajen sauke kaya daga jiragen ruwa cikin hanzari, kuma takan inganta yanayin sufurin kasar.

Image caption Wasu kwantainoni a tashar ruwa ta kan tudu ta Kaduna

Tashar gabar teku ko ta kan tudu?

Akwai rudani game da banbancin tashar ruwa ta kan tudu da tashar sauke kayayyaki ko kwantainoni.

Akan gina tashar sauke kaya ne a yankunan tudu, kuma bayan an sauke kaya daga cikin kwantaina, akan dawo da ita tashar domin 'yan kasuwa su yi amfani da ita wajen zuba kayan da suke bukatar fitarwa kasashen waje.

Amma tashar ruwa ta tudu kuwa wata tsararriyar cibiya ce ta da aka gina domin ta tallafa wa tashar jirgin ruwa da ke gabar teku ta hanyar samar da dukkan ayyukan da ake yi a tashar jirgin ruwan da ke can wani wuri a cikin kasar.

Tashar da shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar ranar Alhamis a Kaduna, tashar kan tudu ce.

Za ta samar da duk ayyukan da ake yi a babbar tashar jirgin ruwa da ke birnin Legas.

A takaice, wannan tashar za ta kawo gagarumin sauki ga tashoshin jirgin ruwan Najeriya, domin da zarar kayan arewacin Najeriya sun isa babbar tashar jirgin ruwa ta gabar teku, sai kawai a wuce da kayan zuwa waccan tashar ta kan tudu, inda masu kayan za su je don karbar kayansu.