'Yan Madrid da za su buga wasa da Numancia

Real Madrid Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bale zai buga karawar domin ya murmure kafin wasan da kungiyar za ta yi a La Liga

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasa 19 da za su buga wa kungiyar fafatawar da za ta yi da Numanci a gasar Copa del Rey a ranar Alhamis.

Numancia ce za ta karbi bakuncin Real a karawar farko a zagayen kungiyoyi 16 da suka rage a wasannin.

Real za ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar 10 ga watan Janairun 2018.

A karawa biyu baya da suka hada, Real ta doke Numancia 4-3 a ranar 14 ga watan Satumba a Bernabeu, sannan ta ci 2-0 a gidan Numanci a ranar 31 ga watan Janairu.

Ga 'yan wasan da za su buga wa Real karawar:

Masu tsaron raga: Navas, Casilla da Moha.

Masu tsaron baya: Carvajal, Vallejo, Varane, Nacho, Theo, Achraf da kuma Tejero.

Masu wasan tsakiya: Casemiro, Marcos Llorente, Asensio, Isco, Kovacic da kuma Ceballos.

Masu cin kwallo: Bale, Lucas Vázquez da kuma Borja Mayoral.

Labarai masu alaka