BBOG: 'Sauran 'yan matan Chibok za su fito'

Kungiyar Bring Back Our Girls
Image caption Kungiyar Bring Back Our Girls ta dade ta na gangamin kiran gwamnati ta kubutar da 'yan matan na Chibok, tun lokacin mulkin tsohon shugaban Nigeria Goodluck Jonathan

Kungiyar nan mai fafutuka da matsawa gwamnatin Nigeria lambar ganin an kubutar da 'yan matan Chibok ta ce ba za su gaji ba har sai sauran matan sun kubuta daga hannun Boko Haram.

Daya daga cikin 'yan kungiyar ta Bring Back Our Girls Morocco Ibrahim, ya shaidawa BBC cewa wannan labari ne da ya sanya su farin ciki, tare da godewa gwamnati kan kokarin da take yi na kubutar da 'yan matan.

Ya kara da cewa, kungiyar su ba za ta gajiya ba har sai lokacin da aka kubutar da dauran 'yan matan 112 da suka rage hannun mayakan na Boko Haram.

A jiya ne dai Kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole mai yaki da kungiyar 'yan ta-da-kayar-baya ta Boko Haram, Manjo Janar Nicholas Ibe Rogers ya ce dakarunsa sun kubutar da wata 'yar makarantar sakandaren Chibok wadda ta shafe kusan shekara 4 a hannun Boko Haram, a ranar Alhamis.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da manema labara na rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an gano yarinyar ne a garin Pulka da ke jihar Borno.

A cewar sanarwar, "Zuwa yanzu, kwarya-kwaryar binciken da aka yi ya nuna cewa yarinyar, mai suna Salomi Pagu ita ce ta 86 cikin jerin 'yan matan Chibok da aka sace wadanda aka wallafa sunayensu a shafin intanet".

Ganawar Buhari da 'yan matan Chibok a hotuna

Musayar matan Chibok: Anya ba za a bar baya da ƙura ba?

A lokacin da aka gano ta tana tare da wata yarinya mai suna Jamila Adams, mai kimanin shekara 14 da kuma wani jariri kuma yanzu haka sojoji suna kulawa da su tare da ba su magunguna, in ji sanarwar.

Wannan ne karon farko da aka gano wata 'yar Chibok tun bayan wadanda aka sako a watan Mayun shekarar 2017.

A wancan lokacin, 'yan matan sun gana da Shugaba Muhammadu Buhari sa'o'i kadan kafin tafiyarsa jinya Birtaniya.

Labarai masu alaka