''Mutane 40,000 sun rasa gidajensu a Benue'

Fulani makiyaya
Image caption A karshen shekarar da ta gabata ne gwamnatin jihar Benue ta dauki matakin haramta yin kiwo ga makiyaya a cikin gari da sanya tara ga wanda aka samu da take dokar

Hukumomin jihar Benue a Nigeria sun ce tashin hankalin da ya faru a makon da ya wuce tsakanin Fulani makiyaya da Manoma ya janyo mutane sama da Dubu 40 sun bar muhallansu.

Shugaban hukumar kai daukin gaggawa ta jihar Samuel Shior, ya ce tuni aka bude sansanin 'yan gudun hijira 4 dan tsugunar da mutanen, wasu an yi amfani ne da makarantun Firamare na gwamnati da ke yankin.

Akalla an hallaka mutane 20 a lokacin da rikicin ya barke tsakanin musulmai Fulani makiyaya dauke da muggan makamai, da kuma kiristoci manoma kan batungonakin kiwo.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun ce adadin wadanda suka mutun ya yi 20. Wannan tashin hankali dai ya fusata mutanen jihar inda suka cika titunan birnin Makurdi dan nuna rashin jin dadi kan lamarin da kiran gwamnati ta dauki mataki kan haka.

A bangare guda kuma, shugaban Nigeria Muhammad Buhari, ya yi Allawadai da tashin hankalin, inda ya kira fadan da na tsagwaron mugunta ne da rashin tausayi.

Ya kuma sha alwashin daukar mataki dan magance matsalar da ta ki ci ta ki cinye, wadda ke haddasa asarar rayuka da dukiya.

Sama da shekara 10 kenan, ake rikici tsakanin Musulmi makiyaya da manoma mabiya addinin Kirista akan batun gonaki na yin kiwo.

Labarai masu alaka