Nigeria: An tura jiragen dauko 'yan ci-rani daga Libya

'Yan ci-ranin Afirka
Image caption Ana amfani da tsofaffin kwale-kwale wajen ketarar da 'yan ci-ranin, a kuma cika shi makil da mutane lamarin da kan haddasa kifiyewarsa a tsakiyar teku

Gwamnatin Nigeria za ta tura karin jiragen da za a dauko 'yan kasar da ke kasar Libya.

A lokacin da ya kai ziyara birnin Tripoli, ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama, ya ce tuni gwamnati ta yi hayar jirage guda biyu dan daukar mutane kusan 800 cikin kwanaki masu zuwa.

Yawancin 'yan ci-ranin da ba su da cikakkun takardun tafiye-tafiye dai 'yan Nigeria ne da ke kokarin ketarawa kasashen turai ta amfani da kasar Libya.

Masu gadin teku da kungiyoyin masu dauke da makamai sun taka rawa wajen hana yawancin 'yan ci-ranin yin tafiyar kasadar tun a watan Yulin bara.

Wani rahoto da kafar yada labarai ta CNN ta nuna a baya-bayan nan, shi ne ya bayyana yadda ake saida wasu daga cikin mutanen a kasar Libya tamkar wasu bayi.

Lamarin da ya fusata yawancin kasashen nahiyar har akai ta gudanar da zanga-zanga kan hakan.

A watan Nuwamba ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ana sayar da 'yan kasar tamkar awaki a Libya.

Da yake jawabi ga 'yan Najeriya mazauna kasashen waje a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, shugaba Buhari ya sha alwashin rage yawan 'yan kasar da ke yin ruguguwa wajen zuwa Turai.

Kungiyar tarayyar Afrika dai ta amince ta kwashe kimaniin 'yan cirani 15,000 daga Libya kafin karshen 2017, amma hakan ba ta samu ba.

Yanzu dai kowacce kasa ta dage da tura jiragen sama dan kwaso 'yan kasashen da suke cikin ukuba a inda ake tsare da su a kasar ta Libya da suka ce da hadin bakin 'yan kasashensu da larabawa ake yin cinikinsu.

Labarai masu alaka