Saudia: 'Yan sarauta na bore kan kudin lantarki da ruwa

Batun biyan kudin ruwa da wutar lantarki ne ya janyo boren
Image caption Masarautar Saudiyya ta ce ba za a amince da mataki irin wannan ba, dan haka dukkan wadanda lamarin ya shafa an cafke su

Wasu 'ya'yan masarautar Saudiyya da ake zargin sun kitsa wata zanga-zanga a fadar kasar da ke Riyadh sun shiga hannun hukuma, inda ake tsare da su a wani gidan kaso mai cike da matakan tsaro a kasar.

Da ya ke tabbatar da kama 'yan sarautar, mai shigar da kara na gwamnatin Saudiyya Sa'oud al-Mujeeb ya ce babu wanda ya fi karfin doka a kasar.

Wakilin BBC birnin Riyadh, ya ce kamar yadda gwamnatin Saudiyya ta bayyana, Yarimomin na bore ne akan abubuwa biyu, sun fusata ne saboda an ce za su fara biyan Kudin ruwa da wutar lantarkin gidajensu.

Sannan sun bukaci a biya su kudin diyya dan uwansu da aka hallaka a bara, bayan tada hayaniya kuma suka ki barin gidan sarautar shi ne aka kama su.

A watan Nuwambar bara, ne dai Muhammad Salman binAlbdul'azeez al-So'oud ya fara gangamin yaki da cin hanci da rashawa a kasar.

Yarima mai jiran gadon dai ya sha alwashin yaki da tsattsauran ra'ayin addini a Saudiyya, da tashi tsaye wajen yakar cin hanci da rashawa da ake zargin ya yi wa masarautar katutu.

Wasu 'yan kasar Saudiyya dai sun yi marhabin da matakin yaki da cin hanci da rashawa da aka kaddamar.

Kuma da yawa daga cikin 'yan kasar na fatan cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden da aka kwato don yin ayyukan da za su amfani al'umma.

Labarai masu alaka