Ana bata wa Fulani suna ne kawai —Miyetti Allah

Fulani and herd Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin Fulani makiyaya da kai hare-hare a kan al'ummu da dama a yankin tsakiyar Najeriya

Kungiyar Miyetti Allah a Najeriya ta ce zargin da ake yi cewa wasu Fulani makiyaya ne suka kai hari a kauyen Rhobi na karamar hukumar Lau a Jihar Taraba labarin kanzon kurege ne kawai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban reshenta na jihar Lagos, Alhaji Abdullahi Lele.

"Bata musu suna ake yi. Don wasu ne ke shigar Fulani suna ta'addanci, sai a ce Fulani ne".

Ya kara da cewa: "Saboda rashin kaunar da ake nuna wa Fulani a Najeriya, duk inda suke a takure suke".

Al'ummar kauyen na Rhobi da ke arewa maso gabashin Najeriya dai sun yi zargin cewa wasu Fulani makiyaya ne suka far wa garin nasu ranar Asabar, inda aka kashe mutum 25 sannan aka jikkata wasu da dama.

Rahotanni dai na cewa akwai garuruwa fiye da guda biyar da ke karamar hukumar ta Lau inda ake samun irin wannan rikici.

Felix Manthly Ubandoma shugaban matasa ne a kauyen na Rhobi, ya kuma shaida wa BBC cewa: "Kawai sai ga Fulani a kan mutanenmu. Aka fara harbi, kuma ana sa wuta a gidajen mutane."

Mista Manthly ya kara da cewa wadanda suka gudu ma ba su tsira ba. "Wadanda suka gudu ma sai a bi ka da mashin a je a harbe ka."

Ya kuma ce an kashe mutane masu yawa, "A yanzu [gawarwakin] da muke da su sun kai 25 a kasa."

Martanin jami'an tsaro

Alhaji Abdullahi Lele dai ya ce kungiyarsu ta Miyetti Allah na kokarin shawo kan lamarin, ko da yake, a cewarsa, Fulani ba sa samun taimako ko kariya daga gwamnati.

"Har yanzu ba mu ga gwamnati ta dauki mataki ko daya ba wanda ke amfanar makiyaya. Babu wurin kiwo, ba a taimaka musu da komai", sannan ya kara da cewa, "ana kashe su kamar kiyashi".

Rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba dai ta ce tana sane da rikicin kuma yanzu haka ta dauki matakan dakile shi.

Mai magana da yawun rundunar David Misal ya ce: "Mutum sun kai hudu wadanda muka tabbatar sun mutu, kuma wadanda suka jikkata an riga an kai su asibiti".

Da aka sanar da shi cewa wasu mazauna kauyen na Rhobi sun ce mutum fiye da ashirin ne suka mutu, sai ya ce: "Ina mai tabbatar maka da cewa wannan lambar da ake fadi ba haka ba ne".

Labarai masu alaka