Taal Old Stars Unity Competition 2018 Lafia, Nasarawa State

Taal Old Stars Unity Competition 2018 Lafia, Nasarawa State

A ranar juma'a aka buga wasan karshe a gasar tsoffin 'yan wasan tamaula wato Taal Old Stars Unity Competition wadda hukumar kwallon kafa ta jihar Nasarawa ta kirkiro domin sada zumunci tsakanin tsoffin 'yan wasan jihar.

Ahmad Wakili Zariya ya hallarci gasar wadda Nagoda Maidoya ta lashe kofin a bugun fenariti, bayan da ta tashi 2-2 da kungiyar Dan'azumi a fafatawar da suka yi a babban filin wasa da ke Lafiya a jihar ta Nasarawa.