Trump: 'Ba zan bude sabon ofishin Amurka ba'

Shugaba Trump ya soke ziyarar da zai kai a watan Fabrairu Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Shugaba Trump ya soke ziyarar da zai kai a watan Fabrairu

Shugaba Donald Trump ya ce ba zai ziyarci Birtaniya a watan gobe ba inda za a kaddamar da sabon ofishin jakadancin Amurkar a Landan.

A cewarsa tashin ofishin jakadancin ba zai amfani kasarsa ba.

A wani bayani da ya yi a shafinsa na twitter, Mr Trump ya dorawa gwamnatin Barack Obama laifi inda ya ce ta siyar da tsohon ofishin jakadancin da araha sanna ta kashe makudan kudade wajen gina sabon ofishin.

A na sa ran Sakataren harkokin wajen Amurkar, Rex Tillerson ne zai wakilce shi a wajen bikin bude ofishin.

Labarai masu alaka