Ba za mu bai wa Fulani wurin kiwo ba — Gwamnan Benue

Samuel Ortom Hakkin mallakar hoto BENUE STATE GOVERNMENT

Gwamnatin jihar Benue State da ke arewacin Najeriya, Samuel Ortom, ya ce jiharsa ba ta da wurin da za a ware wa Fulani makiyaya domin su rika yin kiwon daddobinsu.

Gwamnatin tarayya ce dai ke fafutikar ganin an samar wa Fulanin wurin kiwo da zummar magance rikicin da ke faruwa tsakanin su da manoma a jihohi daban-daban.

Gwamna Ortom ya shaida wa manema labarai a Abuja ranar Litinin cewa "kamar yadda na fada muku kwanakin baya, ban fahimci abin da ake kira wurin da za a yi kiwo ba. A jihar Benue ba mu da hecta 10,000 wacce za a ware domin bai wa makiyaya su yi kiwo."

"Wasu jihohin suna da filyae da kasa amma a Benue ba mu da su; don haka ne muka yi dokar da za ta hana kiwon-sake ga kowa da kowa."

Gwamnan na yin wadannan kalamai ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyya ke neman hanyar da za a samar wa Fulani makiyaya filayen da za su rika yin kiwo.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan da sauran masu ruwa da tsaki a jihar domin lalubo hanyoyin magance rikicin Fulani da manoma.

Rikicin, wanda ake dora alhakinsa kan makiyaya, ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, ko da yake sun sha musanta zargin da ake yi musu.

Fulanin sun ce sau da dama ana kashe su da dabbobinsu ba tare da an hukunta mutanen da suka yi laifi ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana zargin Fulani da kashe-kashe, sai dai sun musanta.

Labarai masu alaka