An tura sojoji neman Turawan da aka sace a Kaduna

An sace Amurkawa biyu da 'yan Canada biyu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An tura dakaru daga Abuja domin gano Turawan da aka sace a Kaduna

Sojojin Najeriya sun shiga aikin neman wasu Amurkawa biyu da 'yan Canada biyu da aka sace a Kaduna.

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance ba suka sace Turawan guda hudu kan hanyar Abuja kusa da garin Jere da ke cikin Jihar Kaduna.

'Yan bindigar sun sace Turawan ne bayan sun kashe 'yan sandan Najeriya biyu da ke ba su kariya.

Tuni dai rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce tana kokarin gano Turawan a raye tare da kama 'yan bindigar da suka sace su.

Wata majiyar soji ta ce an tura dakaru na musamman daga Abuja domin taimakawa 'yan sanda gano Turawan.

Babu dai wani bayani da ya fito daga ofisoshin jekadancin Amurka da Canada a Najeriya game da Turawan da aka sace.

Amma ma'aikatun harakokin wajen kasashen biyu sun shaida wa kamfanin dillacin labaran AFP cewa sun samu labarin sace 'yan kasashensu kuma suna tattaunawa da hukumomin Najeriya domin kubutar da su.

Najeriya dai na fuskantar yawaitar sace-sacen mutane musamman jami'an gwamnati da 'yan siyasa da 'yan kasashen waje domin neman kudin fansa.

A watan Fabrairun bara an taba sace wasu Jamusawa guda biyu, kafin daga bisani aka sake su. Haka ma a watan Oktoban da ya gabata an sace wasu Turawan Birtaniya a yankin Neja Delta inda aka saki uku, bayan an kashe daya daga cikinsu.

Labarai masu alaka