Birtaniya za ta rika jigilar sojin France a yankin Sahel

Britaish PM Theresa May Hakkin mallakar hoto Reuters

Birtaniya za ta aika da taimakon jiragen sama masu saukar ungulu zuwa yankin Sahel na Afirka domin taimakawa kokarin faransa na yaki da ta'addanci a yankin.

Wannan matakin ya biyo bayan wasu yarjejeniyoyi da kasashen biyu suka kulla ne.

Faransa dai na da kusan dakarun soji 4,000 a yankin Afirka ta yamma da ke aikin yaki da masu tada kayar baya.

A cikin jiragen yakin da Birtaniyar za ta aiko da su, akwai samfurin Chinook (shi-NUHK) masu saukar angulu bayan wasu manyan jirage masu jigilar kaya.

Da alama jiragen za su rika jigilar sojojin Faransa ne saboda babu sojin Birtaniya da za su isa yankin.

Faransa ce ke kan gaba wajen yaki da 'yan ta'adda a yankin - inda ta jibge dubban sojojinta suna ayyuka tare da sojojin kasashen yankin.

Wurin da batun ya fi tsnanni shi ne kasar Mali, wanda ya zama wata matattarar masu tada kayar baya.

Akwai gomman kungiyoyi dauke da makamai a kasar - ko wannensu na da nasa bukatar - lamarin da ya jagula zaman lafiya a kasar.

Amma kungiyoyin - kamar JNIM masu alaka da kungiyar Al Qaida na kai hare-hare akai-akai wanda ke janyo damuwa matuka a bagaren gwamnatin kasar da masu mara mata baya.

Ban da dakarun Faransa, akwai wata runduna ta yankin Sahel mai sunan G5 Sahel da MINUSMA - wato sojojin MDD wanda ke da shalkwata a Mali.

Amma girman yankin ya sa ana shan wahala wajen sintirin da dakarun ke yi.

Sannan zafi da yashin hamada sun kasance abokan gabar jiragen yakin kasar Holland da na Jamus da ke yankin - wadanda MDD ta tura domin suma su taimaka wa yakin.

Su ma jiragen na Birtaniya samfurin Chinook zasu taras da wannan matsalar ta na jiran su a daidai wannan lokaci da zasu kama aiki na tabbatar da tsaro.