An kirkiri sabuwar hanyar gane cutar daji

Gwajin zai iya gano cutar sankarar mama Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Gwajin zai iya gano cutar sankarar mama

Wasu masana ilimin kimiyya a Amurka sun ce sun samu gagarumin ci gaba wajen kirkiro wani gwaji na musamman domin gane cutar daji wato kansa.

Masu bincike, sun yi gwajin ne a kan marassa lafiya dubu daya domin ganin ko za a iya gano ire-iren cutar guda takwas.

Gwajin wanda a ka yi wa lakabi da suna CancerSeek ya nuna samun nasara da kashi saba'in cikin dari. Wasu masana sun ce wannan ci gaba na da matukar amfani, sai dai akwai bukatar kara tabbatar da sahihancinsa.

Wasu masana ilimin kimiyya a Amurka sun ce sun dau wani babban mataki wajen kirkiro wani gwaji na musamman domin gane cutar daji wato kansa.

Masu bincike a jami'ar Johns Hopkins sun ce sakamakon abun farin ciki ne kuma zai yi babban tasiri wajen mace-mace a dalilin cutar daji. Burinsu shi ne a rika yin wannan gwaji duk shekara domin a ceto rayukan mutane.

Labarai masu alaka