Dan siyasar Zimbabwe ya mutu a hadarin jirgi

Roy Bennett ya dade ya na sukar gwamnatin Shugaba Mugabe Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Roy Bennett ya dade ya na sukar gwamnatin Shugaba Mugabe

Fitaccen dan siyasar nan na Zimbabwe Roy Bennett ya rasu a hadarin jirgi mai saukar ungulu a Amurka.

Kafin rasuwarsa, Roy Bennett jigo ne a jam'iyyar adawa ta Movement for democratic change. Mr Bennett mai shekaru 60 da matarsa Martha sun rasu a wani yanki mai tsaunuka a New Mexico.

A shekarar 2010 ne aka wanke Mr Bennet daga laifin cin amanar kasa, bayan da a ka yi zarginsa da shirya juyin mulkin Shugaba Robert Mugabe.

Ya yi gudun hijira na rajin kai a Afirka ta kudu inda ya ci gaba da sukar gwamnatin Mr Mugabe.

Labarai masu alaka