'Yaran Afirka sun fi na Turai dogon buri'

'Yaran Afirka sun fi na Turai dogon buri'
Image caption Koyarwa na daya daga cikin ayyukan da aka fi kauna a wasu kasashe.

Wani bincike ya gano cewa, yaran da ke zaune a kasashe maso tasowa sun fi na Burtaniya buri mai kyau a kan aikin da za su yi idan sun girma.

Yawancin yara mazan da ke zaune Burtaniya babban burinsu shi ne su zamo 'yan wasan kwallon kafa ko kuma wasu fitattu da za a sansu a YouTube, yayin da takwarorinsu na Uganda ko Zambia kuwa babban burinsu shi ne su zamo Likitoci ko Malaman makaranta.

An gudanar da wannan bincike ne a kan yara dubu 20, wanda wata cibiya da ke nazari a kan ci gaban matasa ta gudanar.

Kazalika an gudanar da binciken ne ta hanyar tambayar yara 'yan shekara bakwai zuwa 11 a kasashe 20 inda suka fadi abin da suke su zama a rayuwarsu idan sun girma.

Cibiyar ta ce sakamakon ya nuna yawan raina kokarin wani jinsi tun daga yarinta da ake da shi.

Image caption Yara Maza sun fi son zama masana kimiya

A Birtaniya, yawanci yara mata sun fi son zama Injiniyoyi ko masu ilimin kimiyya.

To amma, ayyukan kamar na malaman jinya ko mawaka ko kuma masu gyaran gashi na daga cikin ayyukan da suka fi so.

Labarai masu alaka