Cin zarafin mata ya zama annoba

Paparoman ya kai ziyara wasu kasashen yankin Latin America Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Paparoman ya kai ziyara wasu kasashen yankin Latin America

Paparoma Francis ya bayyana damuwarsa a kan abunda ya ce annoba ce ta cin zarafin mata a Latin Amurka yayin wata ziyara da ya kai Peru.

Lokacin da ya ke magana a wani taron addini a arewacin birnin Trujillo, Paparoman ya ce kamata ya yi a ce mabiya addinin kirista sun yi yaki da cin zarafin mata.

Paparoman ya ce zin carafin mata ya hada da duka, da fyade da kuma kisan kai.

Ya ce mata da dama da a ka ci zarafinsu ba sa iya fitowa su fadi.

An taba yi wa Paparoma gwajin hankali

Jaruman Hollywood sun goyi bayan wadanda a ka yi wa cin zarafi

Ana yi wa masu fyade sassauci — Aisha Buhari

Labarai masu alaka