Turkey ta nemi goyon bayan NATO

Tankokin yakin Turkiyya sun shiga Syria ranar Lahadi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tankokin yakin Turkiyya sun shiga Syria ranar Lahadi

Wakilin Turkiyya na kungiyar tsaro ta NATO, Ahmet Berat Conker ya yi kira ga sauran mambobin kungiyar da su mara ma gwamnatinsa baya a babban farmakin da ta kai don kawar da Kurdawa 'yan bindiga a Syria.

Ya ce abunda gwamnatin kasarsa ke yi bai zarce ka'ida, dan haka abunda su ke bukata daga kasashen duniya da kuma mambobin kungiyar NATO shi ne dole su mara musa baya.

Ya kuma ce goyon bayan da Amurka ke bai wa Kurdawa na kungiyar 'yan bindiga ta YPG a matsayinta na mai yaki da kungiyar IS ya sa Kurdawan zama babbar barazana ga Turkiyya.

Amurka dai na bukatar hadin kan Turkiyya domin ganin farmakin bai dauki tsawon lokaci ba. Kwamitin sulhu na MDD zai yi zaman gaggawa a kan lamarin a yau litinin.

Labarai masu alaka