Cutar Lassa ta hallaka mutum 16 a Nigeria

Ma'aikatan lafiya na cikin wadanda suka rasa rayukansu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikatan lafiya na cikin wadanda suka rasa rayukansu

Hukumomin lafiya a Nigeria sun ce mutane akalla sha shidda ne suka mutu ciki har da ma'aikatan lafiya uku a sakamakon zazzabin Lassa a kasar.

Akwai kuma wasu gwamman mutanen da ke kwance a asibitoci sakamakon kamuwa da cutar, wadda ake dauka daga beraye, kuma mutane ke yada wa juna.

Ma'aikatar lafiya ta Nigeria ta ce cutar ta watsu a jihohi goma, amma ta fi yaduwa ne a jihohin Ebonyi, da Ondo da kuma Edo.

Ta ce tana aiki tare da hukumar lafiya ta duniya da kuma cibiyar yaki da cututtuka ta Amurka akan yadda zaa dakile yaduwar cutar.

Hukumomin kasar sun yi kira alummar kasar akan su tsabtacce muhalinsu.