'Yan tawayen FARC sun kaddamar da yakin neman zabe

FARC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsohon shugaban 'yan tawayen, Rodrigo Londono ne dan takarar jam'iyyar

Kungiyar 'Yan tawayen FARC a Colombia ta kaddamar da yakin neman zabe na farko a matsayin jam'iyyar siyasa domin shiga zaben 'yan majalisa da na shugaban kasa.

Dan takarar kungiyar kuma Tsohon shugaban 'yan tawayen, Rodrigo Londono da ake kira Timochenko ya yi alkawalin yakar talauci da rashawa.

Sannan manufofin 'yan tawayen sun hada da ilimin jami'a kyauta da kyautata kiwon lafiya ga 'yan kasa.

Sai dai kuma 'yan colombia yawanci na tuna barnar da 'yan tawayen ne suka aikata, ta garkuwa da hare hare a rikicin kasar da aka dauki tsawon lokaci ana yi, kafin a sasanta, shekaru biyu da suka gabata.

Kungiyar ta FARC ta shafe shekaru tana gwagwormaya da makamai kafin ta saka hannu kan yarjejeniyar tsagaita buda wuta tsakaninta da gwamnatin kasar.

A 2016 ne 'Yan tawayen kungiyar FARC a Colombia suka sanar da kawo karshen yakin da suke yi na sama da shekaru 50.

Labarai masu alaka