An kubutar da 'yan Afirka ta kudu da aka sace a Nigeria

Kaduna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Matsalar satar mutane ta zama ruwan dare a Najeriya

Rundunar 'Yan sandan Najeriya ta ce ta kubutar da wasu 'Yan Afirka ta Kudu biyu da aka sace su a wani wurin aikin hakar ma'adanai cikin kauyen Maidaro a jihar Kaduna.

Wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar 'yan sandan kasar ta fitar, ta ce sai da jami'an tsaro suka yi amfani da jirgi mai saukar Ungulu da wasu 'yan sanda na musamman kafin cimma sako mutanen guda biyu.

Mutanen da aka kubutar sun hada daThomas Arnold Pearce da Mista Hendrik Gideon bayan sace su a ranar Talata 23 ga watan Janairu a kauyen Maidaro.

Sanarwar kuma ta ce an sako mutanen ne ranar asabar ba tare da wani rauni a jikinsu ba.

Sai dai rundunar 'yan sandan ba ta yi bayani ba ko sai da aka biya kudin fansa kafin a sake su ba.

Al'amarin dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan kubutar da wasu turawa 'yan Amurka biyu da kuma 'yan Canada biyu da aka sace a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Satar mutane dai don neman kudin fansa na kara zama ruwan dare a Najeriya, domin har mutanen karkara ma ba su tsira ba.

Labarai masu alaka