Me ya sa Jay-Z da Trump ba su dasawa?

Jay-Z da Trump Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jay-Z ya dade yana adawa da Trump

Shugaban Donald Trump ya mayar wa Jay-Z da martani bayan mawakin na Amurka ya bayyana shi da cewa "kamar kudin cizo ne da ba ya jin magani".

Jay-Z ya soki Trump ne domin nuna rashin jin dadinsa da yadda shugaban ke nuna wariya ga Amurkawa tsiraru.

A sakon martani da ya wallafa a shafin Twitter, Mista Trump ya ce " alkalumman da aka ruwaito sun nuna ba a taba samun raguwar rashin ayyukan yi tsakanin bakaken fata ba kamar yanzu".

An samu raguwar rashin ayyukan yi ga Amurkawa bakaken fata da kashi 6.8, adadi mafi kankanta da aka taba samu.

Sai dai kuma wasu da ke sukar gwamnatin Trump sun ce ci gaban ya samo asali ne tun a gwamnatin toshon shugaban kasa Obama, kuma rashin ayyukan yi ga bakaken fata ya fi yawa fiye da fararen fata.

A Kafar CNN Jay-Z ya mayar da martani da cewa mayar da hankali ga batun matsalar rashin ayyukan yi ba shi ne abin dubawa ba.

Ya ce ba kudi ba ne damuwar, domin ba a iya auna girman farin-ciki da kudi. "girmama mutane a matsayin 'yan adam, shi ne ake magana", a cewar Jay-Z.

Mawakin dai ya marawa Barack Obama baya ne a lokacin shugabancinsa, sannan ya fito ya goyi bayan Hillary Clinton da Donald Trump ya kada a zaben 2016.

Labarai masu alaka