Mata Musulmi sun gudanar da ranar Hijabi

Wasu mata musulmi a Liberia suke gudanar da ranar sanya hijabi Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Wasu mata musulmi a Liberia suke gudanar da ranar sanya hijabi

A shekara ta 2013 ne aka kadammar da ranar Hijabi ta mata musulmi wadda ake yi a ranar 1 ga watan Fabareru ta kowace shekara.

Wadanda suka shirya ranar kan gayyato mata daga sassa daban -daban n aduniya da kuma adini su sanya hijabi a yinin wannan rana ,domin fadakar da mutane kan muhimancin sanya hijabi da kuma irin wariyar da musulmi mata suke fuskanta a kasashen duniya da dama.

Wadanda suka gudanar da wannan rana sun rika amfani da hashtag #WorldHijabDay.

Mata musulmi kan fuskanci matsala idan sun sanya hijabi a wasu yankuna na duniya, ko a Nigeria ma an samu wasu batutuwa dangane da kalubalen da matan musulmi suke fuskanta kan hijabi.

Yadda hijabi ya hana wata zama lauya a Nigeria

Boko Haram: Shin za ku goyi bayan hana sa hijabi?

A bara an hana wata daliba zama lauya bayan ta kamala karatunta.

Hukumomin makarantar horas da lauyoyi sun ce sun hana Amasa Firdaus shiga cikin taron yaye lauyoyin ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba