Wahalar fetur ta bude wa wata hanyar samun kudi

Bunburutu
Image caption Ta hanyar bunburutu Uwar biyu ta biya kudin haya da na makarantar yaranta

Kasuwar bunburutu ta sake budewa a Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya bayan da matsalar karancin man fetir ta sake kunno kai.

Masu ababan hawa kan kwashe sa'o'i a gidajen man ba tare da samun biyan bukata ba.

A duk lokacin da ake wahalar man fetir, a lokacin ne kuma kasuwar 'yan bunburutu ke budewa.

A 'yan makwannin baya an samu dan sassauci a babban birnin kasar inda mutane kan shiga gidajen mai ba tare da bata lokaci ba.

BBC ta ci karo da wata matashiya mai shekara 23 wadda take sana'ar bunburutu a Abuja domin samun na abinci.

Matar da ake kira Uwar biyu tana kutsawa tsakanin motoci tana rokon mutane su taimaka su sayi man fetir da take dauke da shi a cikin jarkoki.

An fi sanin maza da wannan sana'ar da ake kira bunburutu ko black market.

Image caption Uwar biyu na samun Naira dubu biyar har dubu goma a rana

Amma Uwar biyu tana sharba gumi tana cewa, ta zamo mace mai kamar maza, duk da alamu sun nuna tana jin jiki.

Ta shaidawa BBC cewa dole ce ta sa ta shiga bunburutu, sana'ar da ta kira mai wahalar gaske.

Ta ce mai gidanta talaka ne kuma tana da yara hudu dukkaninsu maza.

"Bunburutu ba sana'a ce mai sauki ba, Saboda muna shan wahala wajen sayen man da kuma sayar da shi" a cewarta.

Ta kuma ce tun kafin gari ya waye take fita neman sayen man duk da ana korarsu a gidajen man.

Uwar biyu ta ce yanayin da kasa take ciki ne ya sa ta tsunduma harkar Bunburutu.

"A baya ina sayar da gasasshiyar doya da agada to amma sai a yini babu mai saye har doyar ta bushe".

Amma yanzu da alama kakar Uwar biyu ta yanke saka domin kuwa harkar bunburutu ta huce mata takaicinta.

Ta ce wahalar fetir da aka shiga ce ta bude ma ta kofar samun kudaden da ta yi shagalin kirsimeti ita da 'ya'yanta.

"Makwabtana sun yi ma na dariya cewa ba mu da bin da za mu yi bikin kirsimeti da shi kwatsam sai ga wannan wahalar mai, kuma na yi amfani da damar har na sai wa yara na tufafi da takalma".

Ta kuma ce ta wannan sana'a ce ta biya kudin haya da na makarantar yara da ake bin su.

Uwar biyu ta ce a rana tana samun dubu biyar, wani lokaci har dubu goma.

Sai dai ta ce ba ta jin dadin sana'ar saboda haduran da ke tattare da ita.

Sana'ar bunburutu na tattare da hadura da suka hada da yiyuwar gobara sakamakon ajiye mai a gida da kuma fuskantar barazana daga jami'an tsaro kasancewar haramtacciyar sana'a ce a gwamnatance.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana wahalar fetur a Najeriya

Sannan mota na iya kade dan bunburutu sakamakon kai kawo a tuitina.

"Ban taba mantawa wata babbar mota ta yi awon gaba da wata kawata 'yar bunburutu sakamakon tsallaka titi da ta yi bayan wani mai mota ya kira ta ya sayi mai kuma wannan ya yi sanadin ajalinta", a cewar Uwar biyu.

Ko uwar biyu za ta daina wannan sana'a?

Uwar biyu ta ce za ta ci gaba da sana'ar domin da ita take samu a yanzu.

"idan na samu wata sana'ar zan bar wannan saboda ai ba wai ba na yin komai ba a yanzu".

Ana iya samun mata zakakurai irin su Uwar biyu da dama masu jajircewa wajen neman na kai to amma hadarin da ke tattare da wannan sana'a ta bunburutu ka iya fin amfaninta yawa.

Sai dai wasu ka iya cewa idan dai har masu ababan hawa ba za su iya bin layi a gidajen mai ba, to za a iya samun 'yan bunburutu dubbai kamar Uwar Biyu.

Labarai masu alaka