Ba zan yi murabus ba- Zuma

Zuma Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugabannin jam'iyyar ANC na son Zuma ya mika mulki ga Ramaphosa

Shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya yi watsi da bukatar jam'iyyarsa na ya yi murabus daga mukamin na shugaban kasa.

Rahotanni sun ce Jacob Zuma ya ki amincewa ya yi murabus ne bayan da wasu jiga-jigan jam'iyarsa ta ANC suka tunkare shi da bukatar a gidansa da ke Pretoria.

Mista Zuma da ke fuskantar zarge-zangen rashawa na fuskantar matsin lamba da ya yi murabus ya mika mulki ga Cyril Ramaphosa, mutumin da ya gaje shi a matsayin shugaban jam'iyyar ANC a watan Disamba.

Yanzu mataki na gaba shi ne shugabannin Jam'iyyar ta ANC za su gana a ranar litinin, kuma ana sa ran za su tattauna ne kan yadda za a tsige Jacob Zuma.

Sai a badi ne za a gudanar da zabe a kasar, amma ana ci gaba da matsin lamba na ganin shugaba Zuma ya sauka daga kan mulki, yayin da yake fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Masu sharhi sun yi gargadin cewa barin matsalar rabuwar kai a jam'iyyar ANC ta ci gaba, zai yi ma jam'iyyar da kuma tattalin arzikin kasar lahani.

Jiga-jigan jam'iyar ANC na kokarin ganin sun dinke barakar da ta kunu kai a cikin jam'iyar domin kawar da rabuwar kai tare da kare martabarta kafin zabe mai zuwa.

Labarai masu alaka