'Sojoji na kuntatawa mutane a kudancin Kamaru'

Kamaru Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutanen Kamaru na tserewa zuwa Najeriya

Ana zaman dar-dar a yankin da ake magana da harshen ingilishi a Kamaru bayan zargin sojoji da farwa fararen hula da duka tare da kwasar kayayyakinsu a samamen da suka kai da sunan farautar 'yan aware.

Wani dan majalisa daga garin Batibo ya yi zargin cewa sojojin na kwatar kudi hannun mutane, al'amarin da ya tursasawa mazauna yankin tserewa su bar gidajensu.

Mutanen yankin dai na ci gaba da kwarara zuwa garuruwan Najeriya da ke kan iyaka da Kamaru.

Masharhanta dai na ganin rashin tausayin da sojojin ke nuna wa fararen hula na iya kara tunzura mutane ga fafutikar da wasu a yankin da ke magana da harshen Ingilishi ke yi na neman ballewa daga kasar.

A makon da ya gabata ne dai Najeriya da mika wa hukumomin Kamaru shugabannin 'yan a waren, matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da shi.

Hukumomin agaji a Nijeriya sun ce 'yan gudun hijira fiye da dubu arba'in ne suka shiga kasar daga yankin da ke magana da Ingilishi a Kamaru, kuma adadin na ci gaba da karuwa.

Wanan ya biyo bayan dirar mikiya da sojojin Kamaru ke yi kan 'yan aware, da ke fafutikar kafa kasar da ake kira Ambazonia.

'Yan gudun hijirar na Kamaru dai na kwarara ne jihar Benue, da wasu jihohin Kudu maso Kudancin Najeriya da ke kan iyaka da Kamaru.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar sun shaidawa BBC cewa ba za su koma Kamaru har sai sun samu 'yanci ko idan an samu zaman lafiya.

Tun a bara ne rikici ya barke a yankin da ke magana da harshen ingilishi da ke zanga-zangar neman ballewa daga Kamaru.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin cewa za a sami karin dubban 'yan gudun hijira da za su shigo Najeriya daga Kamaru idan rikicin ya ci gaba.

Labarai masu alaka