Rundunar sojin sama za ta kafa sansani a jihar Taraba

Sansanin zai taimaka wajan magance rikici tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma

Asalin hoton, Nigerian Airforce

Bayanan hoto,

Sansanin zai taimaka wajan magance rikici tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma

Rundunar sojin Sama a Nigeriya ta ce zata kafa sansanin jiragen sama a jihar Taraba domin dakile rikici makiyaya fulani da manoma.

Hafsan sojin sama na kasar,Air Marshall Abubakar ya kuma ce zaa kafa wata rundunar soji da zata dauki matakin cikin gaggawa a iyakar da ke tsakain jihojin Nasarawa da kuma Benue.

A cikin wata sanarwa da dauke sa hannu kakakin rundunar sojin sama Air vice Marshall Olatakotunbo Adesanya ta ce sansanin na cikin matakan da hukumomi suke dauka domin magance tashe tashen hankula tsakanin makiyaya fulani da kuma manoma.

A baya dai rudunar sojin sama ta Nigeria ta yi shellar kafa sansanoni a jihohin Akwa Ibom da kuma Kurus Riba, domin magnace matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sasan kasar.