Mun shirya karawa da PSG — Zidane

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ce za ta fara karbar bakuncin Paris St -Germain

A ranar Asabar Real Madrid ta ci Real Sociedad 5-2 a wasan mako na 23 a gasar La liga da suka fafata a Santiago Bernabeu.

Cristiano Ronaldo ne ya ci uku rigis a fafatawar, yayin da Lucas Vazquez da Toni Kroos kowannnensu ya ci dai-dai, ita kuwa Sociedad ta ci kwallo ta hannun Jon Bautista da kuma Asier Illarramendi.

Kocin Real Madrid ya ce nasarar da suka samu za ta kara musu kwarin gwiwar fuskantar Paris St-Germain a wasan cin kofin Zakarun Turai da za su yi a ranar Laraba.

Real Madrid ce za ta karbi bakuncin PSG a wasan zagaye na biyu a filin wasa na Santiago Bernabeu, sannan ta ziyarci Faransa a wasa na biyu a ranar Talata 6 ga watan Maris.

Zidane ya ce ba lalle ba ne su ci PSG kwallaye biyar, amma za su fuskance su da kwarin gwiwa da zai taimaka musu.

Paris St-Germain da Real Madrid sun tashi babu ci a gasar cin kofin Zakarun Turan a ranar 21 ga watan Oktoban 2015, a wasa na biyu, yayin da a Spaniya Real ta ci daya mai ban haushi a ranar 3 ga watan Nuwamba.