An kirkiro manhajar gano kalaman ta'addanci

Amber Rudd ta bayyana cewa manhajar na iya gano kashi casa'in da hudu cikin dari na harkokin IS Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Amber Rudd ta bayyana cewa manhajar na iya gano kashi casa'in da hudu cikin dari na harkokin IS

Gwamnatin birtaniya ta ce ta taimaka wajen kirkiro wani sabon manhaja wacce za ta iya gano abubuwan da su ka kunshi ta'addanci a shafikan yanar gizo sannan ta goge su a take.

Ministar harkokin cikin gidan Birtaniya Amber Rudd, ta je Amurka domin tattauna batun manhajar da kamfanonin fasaha tare kuma da yunkurin rage ta'addanci.

Sabuwar manhajar wacce wani kamfanin fasaha a Landan ya kirkiro na amfani ne da wata ma'ajiya mai girma wacce ta kunshi abubuwan da kungiyar IS su ke sawa a shafukan intanet.

Amber Rudd ta bayyana cewa manhajar na iya gano kashi casa'in da hudu cikin dari na harkokin IS, kuma a na sa ran nan gaba za a kafa dokar da za ta tilastawa kamfanoni amfani da wannan manhaja.

Labarai masu alaka