Kim Jong-un ya yaba wa South Korea

Kim Jong-un ya yaba wa South Kore Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim Jong-un ya yaba wa South Korea

Shugaban Korea ta arewa Kim Jong-un ya ce ya na son ya ci gaba da gyara dangantakarsa da Kudu, bayan ziyarar da manyan jami'an su ka kai a wasannin Olympics.

Kafar yada labarai ta kasar ta ce Mr Kim ya karbi wani rahoto daga tawagar jami'an, ciki kuwa har da kanwarsa bayan da su ka dawo.

Rahotanni sun ce ga wadanda su ke son gagarumar tattaunawa tsakanin Koriya ta arewa da ta kudu, lallai wannan alama ce mai nuna nasara. Ba ko yaushe ba ne za ka ji shugaban Koriya ta arewa ya na yabon koriya ta kudu.

Kafar yada labaran dai bata yi bayani a kan ko Koriya ta arewa ta tura gayyatar tattaunawa ga shugaban koriya ta kudu Moon Jae-in ba.

Labarai masu alaka