'Ana fakewa da dawafi don taba jikin mata'

Holy Kaaba

Asalin hoton, Getty Images

Wani batu da aka yi ta mahawara a kansa a kafar sada zumunta a gabas ta tsakiya a makon nan shi ne yadda wasu mata Musulmai suka yi ta fadin yadda wasu maza ke fakewa da aikin hajji domin taba jikin matan musamman a lokacin dawafi.

Wasu matan Afirka ma dai sun ce sun fuskanci irin wannan al'amari.

Sai dai wasu na ganin zakalkalewar matan ce ta son kutsawa cikin maza ke sa hakan faruwa.

Wakilin BBC a Abuja, Usman Minjibir ya tambayi Dr Sani Umar Rijiyar Lemo domin jin yadda ya kamata matan su gudanar da aikin haji.

"Abu na farko shi ne a lura cewa aikin Hajji wuri ne da ake cundanya tsakanin maza da mata."

Ya bayyana cewa, "Aikin Hajji ne aka yarda maza da mata su rika cudanya".

Da aka tambayi Dr Sani, ko wannan ya na da nasaba da kutse-kutsen da mata ke yi don taba Ka'aba ko Hajral Aswad, sai ya ce wannan batun hak yake.

"Ana samu wasu daga cikin mata da ba su da natsuwa, wadanda ba su da kamun kai."