Nigeria ta kera jirgi marar matuki

Shi ne jirgin farko irinsa da aka kera a cikin Nigeria

Asalin hoton, Buhari Sallau Facebook

Bayanan hoto,

Shi ne jirgin farko irinsa da aka kera a cikin Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani jirgi marar matuki da aka kera a cikin gida, irinsa na farko a kasar.

Jirgin wanda cibiyar kere-kere ta dakarun sojin saman Najeriya ta yi, zai yi amfani wajen yaki da 'yan ta-da-kayar-baya da kuma masu fashi da makami.

Akwai tanadin kera jirgin da yawan gaske, har ma da yiwuwar fitar da shi zuwa ketare.

Najeriya na fama da barazanar tsaro rututu ciki har da ta 'yan ta-da-kayar-baya a arewa maso gabas.

Akwai kuma matsalar matasa masu gwagwarmaya da makamai a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ga kuma rikicin makiyaya da manoma.