An kama likitan bogi a jihar Nassarawa

masu ciki

Asalin hoton, Getty Images

Hukumomi a Najeriya na shirin gurfanar da wani mai maganin gargajiya da ake zargi da safarar jarirai.

Hukumar yaki da safarar mutane ta kasar, NAPTIP ta damke Dr Akuchi ne a 'yan makonnin da suka wuce bisa zarginsa da taimaka wa mata samun ciki na bogi daga bisani kuma ya basu jarirai.

Jami'an hukumar sun zargi likitan gargajiyan da yi wa mata 160 maganin samun ciki na bogi a tsawon shekaru hudu da ya yi yana wannan aiki a wani asibiti da ke jihar Nassarawa.

Wasu daga cikin matan sun shaidawa BBC cewa mutumin ya karbi makudan kudade daga hannunsu.

Hukumar ta NAPTIP ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurafar da Dr Akuchi a gaban kotu.

Yankin kudu maso gabashin Najeriya dai ya yi kaurin suna wajen safarar jarirai, inda ko shekarar 2011 'yan sanda suka kai samame a wani gida da ke Aba a jihar Abia inda suka gano 'yan mata fiye da 30 wadanda ake zargin ana yi mu su ciki domin su sayar da jariransu.