An ci zarafin bakaken fata a bikin sabuwar shekara ta China

china

Asalin hoton, Youtube/CCTV

Wani wasan kwaikwayo da gidan talbijin na China ya nuna don murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar a ranar Alhamis, ya jawo ce-ceku-ce akan yadda aka nuna banbancin launin fata.

A wasan kwaikwayon, wanda aka shirya don nuna alakar 'yan Afirka da China, sai aka sanya wata 'yar yankin Asiya ta shafa shuni fuskarta da kuma manyan mazaunai.

Mutane da dama na daukar yin amfani da kayan kwalliyar da zai mayar da fuskar mutum baka, a matsayin cin fuska sosai.

Bikin sabuwar shekarar, wanda aka saba yi duk shekara ya shahara sosai, kuma kusan mutum miliyan 800 ne ke zuwa kallonsa.

Wasu masu sa ido sun nuna cewa hakan ba zai kasance cin fuska ga 'yan Afirka ba.

Duk da haka, wannan ba shi ne karo na farko da wasannin nishaɗi na China suka haifar da rikici ba, ta yadda ake ganin suna nuna kabilanci da wariyar launin fata.

An fara bikin sabuwar shekarar ne da nuna wata kungiya ta masu raye-raye 'yan Afirka, da kuma mutane da suka yi shiga kamar zakuna da bareyi da jakunan dawa.

Daga nan kuma sai aka gabatar da wasan kwaikwayo inda wata bakar mata ta umarci wani dan China da ya fito a matsayin mijinta ya durkusa a yayin da ya hadu da mahaifiyarta don gaishe ta.

Sai dai a yayin da yarinyar ta kasance baka ce, sai wacce ta fito a matsayin uwar tata ta kasance 'yar China ce amma ta shafa bakin fenti a fuskarta, ta kuma sanya manyan mazaunai na karya, a matsayin tana kwaikwayar yadda halittar 'yan Afirka take.