Trump zai hana amfani da na'urorin karawa bindiga karfin aiki

Na'urar na baiwa bindiga damar yin harbi mai yawa cikin karamin lokaci Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Na'urar na baiwa bindiga damar yin harbi mai yawa cikin karamin lokaci

Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin daukar matakan kawar da na'urori da ke baiwa bindigogi damar yin jerin harbe-harbe a cikin kankanin lokaci.

An bai wa Jami'ai a hukumar shari'a izinin kafa dokar da za ta haramta amfani da na'urorin wadanda a ka yi amfani da su wajen hallaka mutum 58 a Las Vegas a watan Oktobar bara.

A baya an sha yin muhawara kan ko hukumomin gwamnati na da damar haramta amfani da wannan na'ura. Amma a yanzu Shugaba Trump ya ba su izinin yin hakan.

Mr Trump dai ya fuskanci matsin lamba tun bayan da a ka yi harbi a wata makaranta a Florida a makon jiya.

Ya kuma nuna cewa zai goyi bayan sabbin ka'idojin kididdige wadanda za su mallaki bindigogi nan gaba.

Labarai masu alaka