Nigeria; Sojoji sun ceto 'yan matan makarantar Dapchi

Dapchi Hakkin mallakar hoto GGSS

Ana ci gaba da samun rahotanni dangane da batan 'yan matan makarantar sakandaren Dapchi da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya, wadanda ba a ji duriyarsu ba tun bayan da mayakan Boko Haram suka kai hari makarantar a ranar Litinin da yamma.

Tun da farko dai hukumomi sun ce 'yan matan sun bazama daji ne don neman wajen buya yayin da maharan suka dirarwa makarantar.

Wani malamin makarantar ma ya shaida wa BBC cewa mayakan ba su kai harin don sace 'yan mata ba sai don 'satar abinci,' kuma sun saci kayan abincin da dama.

Sai dai gwamnatin jihar Yoben ta tabbatar da rashin bayyanar 'yan matan a ranar Laraba da safe, inda ta ce ba a ji duriyarsu ba, sai dai ana ci gaba da neman su a dazuzzukan da ke kusa da garin.

Amma a ranar Larabar da yamma sojojin Najeriya suka sanar da cewa sun ceto wasu 'yan matan daga hannun mayakan Boko Haram da suka yi awon gaba da su.

Kakakin gwamnan jihar Yobe Abdullahi Bego ya tabbatarwa BBC cewa sojojin Najeriya sun bi 'yan Boko Haram tare da kwato daliban.

Ya ce yanzu haka 'dalibai matan suna hannun sojojin da suka kwato su, kuma nan gaba gwamnatin Yobe za ta yi karin bayani.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya mabato iyayen yaran da jami'an gwamnati na cewa 'yan mata 76 aka ceto, kuma har yanzu akwai 13 da ba a gani ba.

Reuters ya kuma ce an gano 'yan mata biyu da suka mutu, amma ba a bayyana abun da ya yi sanadin kashe su ba.

A ranar Litinin ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari makarantar inda suka yi ta harbe-harbe tare da tayar da abun fashewa.

Rahotanni sun ce maharan sun sace kayayyaki daga makarantar bayan sun tarar wasu daliban da malaman sun tsere.

Labarai masu alaka