Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bincike ya nuna magungunan ciwon da ke sa damuwa na aiki

Masana sun gudanar da wani bincike da ya tabo fannoni da dama a jami'ar Oxford wanda ya musanta bayanan da ke nuna cewa magungunan warkar da ciwon tsananin damuwa ba sa tasiri.

Binciken mai zurfi ya nuna cewa ashirin da daya daga cikin magungunan sun taimaka wajen baiwa marassa lafiya sauki.

Masu binciken sun duba sama da gwaje-gwaje dari biyar kuma sun hada da wasu bayani da aka yi a baya da wasu kamfanonin magunguna su ka ki fitarwa.

Sakamakon da a ka wallafa a wata mujallar kiwon lafiya, The Lancet ya nuna cewa magungunan su na tasiri. Haka kuma, kungiyar likitoci masu kula da masu tabin hankali a Birtaniya ta ce binciken zai kawo karshen duk wani rikici.