Yaran Rohingya na cikin hadari-UNICEF

Kananan yara na cikin hadari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kananan yara na cikin hadari

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi gargadin cewa kananan yara 'yan Rohingya kashi uku bisa hudu na fuskantar babbar barazana har na tsawon wasu shekaru masu zuwa.

An bayyana hakan ne a wani rahoton UNICEF yayin cika watanni shida tun bayan fara rikicin daya tilastawa 'yan Rohingya fiye da miliyan daya tserewa zuwa Bangladesh don gujewa tashe tashen hankula a Myanmar.

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniyar ya ce akwai dubban kananan yara da yanzu haka suke rabe a wasu sansanoni na wucin gadi.

Kuma basa samun ilimi tare da fuskantar hadarin kamuwa da cututtuka da kuma tashe tashen hankula.

Bangladesh ta hana Msulimin Rohingya zuwa ko'ina

Bangladesh 'za ta mayar da Musulmin Rohingya 300' Myanmar

Labarai masu alaka