Amurka za ta bude ofishinta na Kudus a watan Mayu

Kudus
Image caption A watan Disambar bara ne aka kafa tutar Amurka da Israila a birnin Kudus

Ma'aikatar cikin gida a Amurka ta sanar da cewa a watan Mayu mai zuwa ne za ta bude ofishin diflomasiyyarta a birnin Kudus.

Ranar bude ofishin za ta zo daidai da ranar bikin tunawa da kfa kasar Israela shekara 70 da ta wuce kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin kura ta dan lafa, kan takaddamar da ake yi na maida ofishin jakadancin Amurkar birnin Kudus.

Shugaba Donald Trum ya sha alwashin tabbatar da hakan, ko da yake kasashe da dama ciki har da na tarayyar turai sun nuna rahin amincewa.

Wani babban jami'in gwamnatin Falasdinu, Sa'eb Erekat, ya kira matakin na tsokanar fada.

Shugaba Benjamin Netanyahu ya yi murna da sanarwar bude ofishin Diflomasiyyar, ya kara da cewa wannan rana ce mai matukar muhimmanci a tarihin Isra'ilawa.

A shekarar da ta gabata ne dai shugaba Donald Trump ya sanar da maida ofishin jakancin Amurka birnin Kudus, maimakon Tel Aviv.

A yanzu kuma sabon ofishin zai kasance ne a gundumar Arnona da ke tsakiyar Kudus.

Labarai masu alaka