Ta yiwu a tsagaita wuta a garin Ghouta na Syria

Wani yaro da ka kubutar daga ginin da bam ya ruguza a Ghouta
Image caption Kananan yara ne suka fi shan wahala a yakin da ake a Syria

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai kada kuri'a dan dakatar da bude wuta a garin Ghouta na Syria, dan kai agaji ga dubban fararen hula da ke tsananin bukatar taimako.

Kasar Rasha dai na bukatar a samu sauyi a daftarin da ya yi kiran da a samu tsagaita wuta a Syria, domin bayar da damar kai kayan agaji da kuma taimakawa marassa lafiya.

Jami'an diplomasiyya na kasashe waje sun zargi Rasha da, babbar kawar Syria da kawo tsaiko, yayinda kasar Fransa ta ce duk wani yunkuri na bata lokaci zai iya kawo karshen majalisar dinkin duniyar ita kanta.

Hankulan kasashe da dama ya koma kan irin halin matsin da fararen hula ke ciki a gabashin Ghouta, matattarar 'yan tawaye..A jiya Jumma'a jiragen yaki sun kai hare-hare a wurare da dama ciki har da yankunan Hamouriyeh da Douma.

Kasashen yamma dai na zargin Rasha da son a bawa Syria lokaci ta kaddamar da hare-hare a wuraren da yan tawayen suka mamaye da ke Damascus da ma wajen birnin.Amurka da Birtaniya da Fransa sun yi kira da a amince da matakin tsagaita wutar domin kai kayan agajin ba tare da bata lokaci ba.

A jiya jumma'a ne shugaba Trump na Amurka ya dora alhakin matsalar kai kayan gajin da ake fama da ita a Syria akan Rasha da Iran.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Syrian Observatory for human rights ta ce adadin wadanda aka kashe tun daga ranar Lahadin data gabata kawo yanzu ya kai 462, ciki har da yara 99.Yanzu haka dai akwai mutane kusan dubu 393 da suka makale a yankunan da dakarun gwamnatin Syria ke kaddamar da hare-hare kan 'yan tawaye.

Tuni dai gwamnatin Syria ta musanta cewa tana kai wa fararen hula hari, inda ta hakikance cewa tana so ta kawar da 'yan ta'addan da ke zaune gabashin Ghouta ne shi ya sa ta ke kai hare-haren.Hukumomin agaji dai sun ce akwai asibitoci da dama a yankin da tun ranar Lahadin da ta wuce ba a aiki a ciki saboda hare-haren da ake kai wa.

Labarai masu alaka