Yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki a Syria

Rikicin Syria ya fi kowanne dadewa ana yi tun bayan kadawar guguwar sauyi a yankin gabas ta tsakiya sama da shekara 6
Image caption Yara kanana na tsananin bukatar taimako a yankunan da aka yi wa kawanya a Syria

Manyan kungiyoyin 'yan a ware a Syria da ke iko da gabashin garin Ghouta sun amince da matakin tsagaita wuta da kwamitin tsaro na MDD ya jagoranta dan kai kayan agaji ga fararen hula a yankunan da suka kamale a kasar.

Kungiyoyin biyu sun yi alkawarin za su bai wa ayarin motocin agajin kariya, su kuma raka su har sai sun shiga yammacin birnin Damuscus.

Shugaban kungiyar likitocin Amurka a Syria Dr Ahmad Tarakji ya yi maraba da dakatar da bude wutar na wata guda.

Ya kara da cewa tuntuni ya kamata a dauki matakin ina ganin wannan mataki ne mai kyau, fararen hula da ke gabashin Ghouta sun damu matuka kan ko bangarorin za su bada hadin kai a dakatar da bude wutar.

A makon da ya gabata ne dakarun gwamnatin Syrian suka kaddamar da hare-hare a yankunan da 'yan tawayen suke da ke gabashin Ghouta a kusa da birnin Damascus.

Bayan kada kuri'ar amincewar da aka yi a birnin New York, masu fafutuka sun ce an cigaba da kai hare-hare ta sama.

Tun ranar alhamis yakamata ace an kada kuri'ar, amma aka rinka jan kafa kafin a amince.

Rasha wadda babbar kawar Syria ce, na bukatar a samu sauye-sauye, yayinda Jami'an diflomasiyya dake wakiltar manyan kasashen duniya a majalisar dinkin duniya suka zargi Rashan da kawo tsaiko.

Rahotanni sun ce dakarun gwamnatin Syrian sun kashe mutane kusan 500 da ke yankunan da 'yan tawayen suka mamaye a yayin hare-haren da suke kai wa 'yan tawayen, yayinda su kuma 'yan tawayen suka kashe fararen hula 16 a sakamakon bude wutar da suka yi a Damascus.

Ana dai son tsagaita wutar ne na tsawon wata guda domin bayar da damar kai kayan agaji ga mutanen da suka makale a yankunan da 'yan tawayen su ke.

Nan gaba kadan ne dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za su tattauna akan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar tare da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.

Labarai masu alaka