Birtaniya: Bam ya hallaka mutum hudu a Leicester

An girke jami'an tsaron kar ta kwana a kusa da ind
Bayanan hoto,

Wakilin BBC da ke wurin ya ce jami'an tsaro sun yi shirin kar ta kwana a yankin

'Yan sanda a birnin Leicester sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, a lokacin da wani abu ya fashe a wani kanti.

Lamarin ya faru ne a kan titin Hinckley da misalin karfe bakwai na yamma a ranar Lahadi, kamar yadda shugaban 'yan sandan yankin Supt Shanes O'Neil ya bayyana.

'Yan sandan sun ce wasu mutane hudu na kwance a asibiti sakamakon mummunan raunin da suka ji.

Mista O'Neill ya kara da cewa ta yiwu akwai karin wasu ababen fashewar, don haka an girke jami'an tsaron kar ta kwana da ma'aikatan agaji don kar lamarin ya dagule.