'An ci zarafin mata a kudancin Syria'

Yawancin matan na zaune a sansanonin 'yan gudun hijira da yankunan da aka yi wa kawanya
Image caption Yakin da ake a Syria ya raba miliyoyin mutane da muhallansu

BBC ta gano masu kai kayan agaji, da majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji suka wakilta dan shiga kasar Syria sun ci zarafin mata ta hanyar lalata da su.

Kungiyoyin Care da kuma International Rescue Committee, sun yi gargadi kan cin zarafin a shekarar 2015.

Amma rahoton da hukumar kula da yawan al'uma ta majalisar dinkin duniya ta gudanar ya gano ana yin lalata da matan ne sannan a ba su kayan abinci a kudancin Syria.

Sai dai wani ma'aikacin agaji ya yi ikirarin ba su da hurumin bada kayan agaji kai tsaye har sai masu sa ido sun iso.

Binciken da BBC ta yi ta hanyar tuntubar kungiyoyin agajin na majalisar da masu zaman kansu, sun ce sam ba su san takwarorinsu na aiki na gudanar da mummunar dabi'ar.

Nan da lokaci kadan, yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 5 za ta fara aiki a gabashin garin Ghouta na Syria, yankin da 'yan tawaye suka makale.

Rasha ce dai ta bada wannan umarni, ta kuma ce za a dinga tsagaita wuta na sa'o'i 5 a kowacce rana dan fararen hula su samu damar tserewa daga yankin da aka yi wa kawanya.

Ba tabbas ko kungiyoyin agaji za su shiga da kayan abinci da magani garin.

Wani likita da bai so a bayyana sunan sa ba yace babu magani da kayan aiki a asibitin garin, ya yin da likitoci da ke aikin sadaukar da kai su na rayuwa tsakanin rai da ajali.

Likitan ya ce yakin da aka dauki sama da shekara 4 ana yi a Syria, ya sanya daukacin kasar cikin zullumi da tashin hankali. Sannan abin da ke faruwa na shigen kama da labarin yakin duniya na biyu da suka karanta.

Labarai masu alaka