An sake bude cocin Holy Sepulchre a Jerusalem

An sake bude cocin Holy Sepulchre a Jerusalem Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY
Image caption An sake bude cocin Holy Sepulchre a Jerusalem

Shugabannin coci a birnin Kudus sun sake bude cocin Holy Sepulchre a yau Laraba.

Wannan na zuwa ne bayan hukumomin Isra'ila sun dakatar da wani sabon tsarin haraji.

Shugabannin mabiya darikar Roman Catolika da na Greek Orthodox da kuma na cocin Armenia sun soki tsarin ta hanyar rufe wani coci a wajen da kiristoci da dama su ka yadda cewa a nan a ka gicciye Annabi Isa, a nan a ka rufe shi kuma a nan a ka tayar da shi.

Magajin garin Birnin Kudus Nir Barkat ya dakatar da sabon shirin harajin, kuma Piraim minista Benjamin Netanyahu ya kaddamar da wata tawaga domin warware matsalar.

Labarai masu alaka