An ragewa Kushner ikon sanin bayanan sirri

Mr Kushner ba zai rika samun rahotannin sirrin ba daga yanzu Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Kushner ba zai rika samun rahotannin sirrin ba daga yanzu

An ragewa sirikin Shugaba Donald Trump kuma babban mai bashi shawara Jared Kushner karfin ikon sanin bayanan sirri a fadar White House.

Wannan na nufin cewa zai rasa damar sanin wasu abubuwa masu muhimmanci ciki har da rahotannin leken asirin kasar.

Rahotanni sun nuna cewa ana yi wa Jared Kushner lakabi da sakataren komai. Sirikinsa, Shugaba Trump ya sa shi a harkokin wanzar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, ya hada kai da Mexico sannan ya jagoranci tattaunawa da China. Sai dai a yanzu dole ya yi wadannan ayyukan ba tare da sanin bayanan sirrin kasar ba.

Lauyansa ya ce Mr Kushner ya yi duk abunda ya kamata domin samun cikakken ikon sanin bayanan asiri, kuma ya ce wannan sauyi ba zai shafi ayyukansa masu muhimmanci ba.

Labarai masu alaka