Hazo da kankara sun mamaye Burtaniya

Kankara da hazo na janyo cunkoson ababen hawa a yankin Scotland Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kankara da hazo na janyo cunkoson ababen hawa a yankin Scotland

Yanayin hazo da iska hade da ruwan sama da ake yi a Burtaniya sun haddasa tsaiko ga zirga-zirga a wasu sassa na Burtaniya.

A yankin Scotland, muku-mukun sanyi na ci gaba da karuwa a yankin da kuma arewacin Burtaniya inda aka yi hasashen cewa kankara da za ta sauko za ta kai Sentimita 40 a wasu yankunan.

An gargadi jama'a a yankin Scotland da arewacin Burtaniya game da saukar kankara da kuma birnin London hade da wasu yankuna da ke kudu maso gabashin Ingila.

Haka kuma an yi hasashen cewa kankarar za ta ci gaba da sauka a yankin Wales da kuma yammacin Midland tun daga ranar Ahamis har zuwa safiyar Juma'a.

Ofishin kula da yanayi na Burtaniya ya gargadi jama'a musamman matafiya su rika duba hasashen yanayi da ake fitarwa a kai akai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi hasashen cewa muku-mukun sanyi zai karu ranar Alhamis

Labarai masu alaka