Babu kasar da ta kawo karshen yunwa a Afirka

Wasu taswirai da aka buga a mujallar Nature sun nuna bayanan filla-filla a kan batun Hakkin mallakar hoto NATURE
Image caption Wasu taswirai da aka buga a mujallar Nature sun nuna bayanan filla-filla a kan batun

Wani bincike kan samar da abinci da ilimi ga kananan yara a Afirka, ya nuna cewa babu kasar da za ta cimma manufar MDD ta kawo karshen yunwa a rayuwar kananan yara nan da shekaru goma masu zuwa a Nahiyar.

Wasu taswirai da aka buga a mujallar Nature sun nuna bayanan filla-filla a kan batun.

Kasashe da dama musamman ma a Afrika kudu da sahara da kuma yankunan gabas da kudu sun samu ci gaba ta fannin rashin abinci mai gina jiki, a shekarau 15 din da a ka yi a na binciken. Amma a karo na farko, binciken ya nuna dalilin da ya sa akwai babban rashin daidaito a tsakanin kasashe.

Duk da an samu ci gaba a kasashen Afirka da dama a baya baya nan, ciki har da Algeria da Mozambique da Ghana, duk cikinsu babu wacce ta kama hanyar kawar da rashin abinci mai gina jiki musamman a kananan yara nan da shekarar 2023.

Masana sun ce binciken zai yi amfani wajen bayyana inda a ke tsananin bukatar taimako.

Labarai masu alaka