An siyar da zanen dan Nigeria kan £1.2m

A baya bayan nan kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da a ke yi a Najeriya Hakkin mallakar hoto BONHAMS
Image caption A baya bayan nan kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da a ke yi a Najeriya

An siyar da wani zane a kan kudi sama da dala miliyan daya da rabi wanda daya daga cikin kwararrun masu zane na zamani a Najeriya ya yi wanda kuma shekaru kusan arba'in kenan da bacewarsa.

Ben Enwonwu ne ya yi zanen na wata Gimbiya 'yar Najeriya, wanda a ke kira Tutu a shekarar alif dari tara da saba'in da hudu.

Rabon da a ga zanen dai tun a shekarar alif dari tara da saba'in da hudun ne a lokacin da a ka nuna shi a Legas, sai kwanan nan da a ka gano shi a wani gida a arewacin Landan.

A baya bayan nan dai, kasashen duniya na nuna sha'awar zane-zanen da a ke yi a Najeriya kuma darajarsu ta karu.

Labarai masu alaka